Isa ga babban shafi
Rasha-Koriya

Putin da Kim na gudanar da taronsu a Rasha

Shugabannin Kasashen Rasha da Koriya ta Arewa sun fara gudanar da taronsu na farko a birnin Vladivostok wanda zai mayar da hankali kan inganta dangantakar kasashen biyu da kuma bunkasa tattalin arziki.

Shugaban Koriya ta Arewa  Kim Jong-un da shugaban Rasha Vladimir Poutine a birnin Vladivostok
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un da shugaban Rasha Vladimir Poutine a birnin Vladivostok Alexander Zemlianichenko / POOL / AFP
Talla

Bayan faretin ban-girma da aka yi wa shugaba Kim Jong-Un da kuma gabatar da manyan jami’an gwamnatocin kasashen biyu, shugaba Vladimir Putin da bakon nasa sun bayyana aniyarsu ta aiki tare.

Shugaba Putin ya shaida wa Kim cewar, yana goyana bayan shirin rage tankiyar da ake samu a mashigin ruwan Koriya da kuma shirin bunkasa tattalin arzikin a tsakaninsu.

Shugaban na Rasha ya ce, yana da kwarin gwuiwar cewar, ziyarar da ya kai Rashar za ta taimaka musu fahimtar yadda za su magance rikicin da ake samu a mashigin ruwan Koriya da kuma gudumawar da Rasha za ta bayar.

Shi kuwa shugaba Kim cewa ya yi, a shiriye yake ya farfado da dangantaka mai tarihi tsakanin kasashen biyu, inda ya bayyana fatar ganawar za ta basu damar bunkasa dadaddiyar alakarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.