Isa ga babban shafi
ISIS

Jagoran mayakan IS ya bayyana a sabon bidiyo

A karon farko cikin shekaru biyar, Jagoran Kungiyar IS, Abubakar al-Baghdadi da duniya ke nema ruwa a jallo, ya bayyana a wani faifen bidiyo, inda ya tabbatar da fatattakar da aka yi wa mayakansa a Baghouz da ke Syria a cikin watan Maris da ya gabata. Jagoran ya bayyana harin da ya kashe mutane fiye da 250 a Sri Lanka a matsayin ramako kan abinda aka yi wa ‘yan uwansa a Baghouz.

Abubakar  al-Baghdadi da ya bayyana a wani sabon bidiyo
Abubakar al-Baghdadi da ya bayyana a wani sabon bidiyo AFP / AL-FURQAN MEDIA
Talla

A shekarar 2014 ne a birnin Mosul, aka yi wa Abubakar al-Baghdadi ganin karshe, lokacin da ya sanar da kafa daular mayakan IS a sassa da dama na Iraqi da Syria.

A sabon bidiyon da kafar yada labaran IS ta al-Furkan ta fitar a wannan Litinin, al-Baghdadi da ke zaune akan kushin gicciye da kafafunsa, ya ce, an kawo karshen yakin Baghouz, yayinda ya bayyana galabar da aka samu akan kungiyar a wurare da daban daban da suka hada da birnin Mosul na Iraqi da Sirte na Libya , sai dai a cewarsa, mayakan jihadin basu sallama sansaninsu ba.

Jagoran na IS da ya rina dogon gemunsa da lalle, ya ce, All… ya ne umarce su da su yi yaki, amma bai umarce su da lalle sai sun samu nasara ba.

A wani bangare na bidiyon da bai nuna fuskarsa ba, an jiyo muryar al-Baghdadi na cewa, harin ranar bikin Easter da ya hallaka mutane 253 a Sri Lanka tare da jikkata 500, na a matsayin ramako kan farmakin da aka kai wa ‘yan uwansa a Baghouz.

Kazalika jagoran na IS ya ce, hare-haren da suke kaddamarwa kan kasashen Yammaci, wani bangare ne na dadadden yakin da suke yi, kuma za su ci gaba da daukar fansar mayakansu da aka kashe a cewarsa.

Al-Baghdadi ya ce, nan gaba kadan za su kaddamar da wasu sabbin hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.