rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Musulman duniya za su fara azumi a ranar Litinin

media
Saudiya ta ce, babu alamar jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Asabar arabnews

Kwamitin duban wata na Saudiya ya bayyana cewa, babu alamar jinjirin watan Ramadan a wannan yammaci na ranar Asabar, abinda ke nufin cewa, sai zuwa ranar Litinin ne miliyoyin al’ummar Musulmi za su fara azumin Ramadan a sassan duniya.


Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa'ad Abubakar ya bukaci 'yan kasar da su fara duban watan na Ramadan daga gobe Lahadi, 5 ga watan Mayu.

Wani lokaci dai ana samun sabanin ganin watan tsakanin kasashen duniya, abinda ke sa wasu kasashen ke riga takwarorinsu daukar azumin.

Azumtar watan Ramadan wajibi ne ga Musulman da suka kai shekarun balaga , kuma daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar da suka hada da imani da salla da zakka ( ga mai hali) da hajji (ga mai iko).

Al’ummar Musulmi na kame baki da shawa’a tun daga ketowar alfijir zuwa ga faduwar rana a yayin gudanar da azumin watan Ramadan.