rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Korea ta Arewa Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za mu kulla yarjejeniya da Kim- Trump

media
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un REUTERS/Leah Millis

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kwarin guiwar cewa, shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong Un ba zai karya alkawarinsa ba bayan Koriya ta Kudu ta ce, gwamnatin Kim ta sake gwaje-gwajen makamai masu linzami.


A sakon Twitter da ya aika, shugaba Trump ya ce, "kodayake komai mai iya faruwa a wannan duniyar, amma dai ya yi amanna cewa, Kim Jong Un na sane da kyakkayar makomar tattalin arzikin Koriya ta Arewa, a don haka ba zai aikata abinda zai kawo karshen haka ba" a cewar Trump.

Kazalika shugaban na Amurka ya ce, har yanzu, Kim Jong nada masaniyar cewa, suna tare, yayinda ya kara da cewa, akwai yarjejeniyar da za ta kullu a tsakaninsu.

Tun bayan ganawarsu mai cike da tarihi a Singapore a bara, shugaba Trump ke cewa, Kim zai mutunta batun kwance damarar makaman nukiliyar kasar.

Tattaunawar shugabannin biyu a birnin Hanaoi a cikin watan Fabairun da ya gabata, ta tabarbare, abinda ya sa suka tashi baram-baram ba tare da cimma wata matsaya ba.