rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka China Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

China za ta gana da Amurka kan harajin kasuwanci

media
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping Nicolas ASFOURI / AFP

China ta ce, har yanzu tana da aniyar tura tawagarta zuwa Amurka domin tattaunawar kasuwanci da hukumomin Washington, duk da cewa shugaba Donald Trump ya lashi takobin kara kudin haraji kan kayyakin da China ke shigar da su Amurka.


Shugaba Donald Trump ya kara kudin harajin ne a daidai lokacin da wakilan China ke shirin ganawa da hukumomin Amurka a birnin Washington a ranar Laraba mai zuwa, ganawar da ake kallo a matsayin wani yunkuri na karshe da zai kai ga cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu ko kuma ta kara farfado da yakin kasuwanci a tsakaninsu.

A wani sako da aika ta shafinsa na Twitter, shugaba Trump ya ce, zancen cimma yarjejeniyar kasuwanci da China na nan daram, amma dai za a samu jinkiri a cewarsa.

A wannan Litinin ne, Trump ya kara nanata cewa, suna asarar Dala biliyan 500 a harkar kasuwanci da China, in da ya ce, ba za su sake amincewa da haka ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, shugaban na Amurka ya ce, za su kara harajin kashi 25 kan kayayyakin China na Dala biliyan 200, yayinda tuni Amurkar ta fara dora kashi 25 kan kudin fiton da Kwastam ke karba daga wasu kayayyakin fasaha na Dala biliyan 50 da Chinan ke shigowa da su.

Sai dai duk wannan mataki na Trump, mai magana da yawun Ma’aikayar Harkokin Wajen China, Geng Shuang ya ce, a halin yanzu tawagarsu na cikin shirin halartar tattaunawar fahimtar juna da Amurka, sai dai bai sanar da ranar da tawagar za ta isa Washington ba.

A makon jiya ne, tawagar Amurka ta ziyarci Beijing don tattaunawa da hukumomin China, ganawar da Sakataren Baitul Malin Amurka, Steven Mnuchin ya ce, ta yi armashi.