rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Faransa Najeriya Duniyarmu A Yau

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Musulmi a sassan duniya sun soma Azumin watan Ramadan

media
Muslmi a babban masallacin birnin Strasbourg da ke kasar Faransa, yayin gudanar da Sallar Azahar a watan Ramadan. REUTERS/Vincent Kessler

Yau Litinin Al’ummar Musulmi a sassan duniya suka tashi da azumin watan Ramadan, bayan ganin jinjirin wata da yammacin jiya a kasashe da dama.


A Najeriya Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin watan na Ramadan, tare da kuma bayyana Yau litinin a matsayin daya ga watan.

Saudi Arabia ta sanar da cika kwanaki 30 na watan Sha’aban jiya Lahadi, saboda haka ranar yau ta zama ranar 1 ga watan Ramadan.

Azumtar watan Ramadan wajibi ne ga Musulman da suka kai shekarun balag , kuma daya ne daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar da suka hada da Imani da Salla da Zakka (ga mai hali) da Hajji (ga mai iko).

Al’ummar Musulmi na kame baki da shawa’a tun daga ketowar alfijir zuwa ga faduwar rana a yayin gudanar da azumin watan Ramadan.