rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Muhalli Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wasu halittun duniya na fuskantar barazanar karewa

media
Nau'ukan halittun duniya kimanin miliyan 1 na fuskantar barazanar karewa daga doran kasa saboda gurbacewar muhalli Boris HORVAT / AFP

Wani rahoton bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a yau Litinin, ya nuna cewa ayyukan dan Adam da ke lalata muhallinsa na barazanar karar da hallitun dabbobi da na tsirrai daban-daban akalla miliyan daya nan da wasu ‘yan shekaru.


Tawagar kwararru kan kimiyya da muhalli sama da 400 ne suka gudanar da wannan bincike, wanda a cikinsa suka yi gargadin cewa, wani yanki daga cikin jumullar nau'ukan halittun duniya kimanin miliyan takwas suna mutuwa cikin sauri a dalilin gurbatar muhalli, fiye da makamancin hakan da aka taba fuskanta sama shekaru miliyan 10 da suka gabata.

Masanan sun kara da gargadin cewa, mutuwar ire-iren tsirran da dabbobi cikin sauri, ka iya haifar da shafewar hallitu masu yawan gaske cikin gajeren lokaci, kamar yadda hakan ta faru ga manyan dabbobin da suka fi girma a tarihin duniya, da a turance ko a kimiyyance ake kira da Dinosaurs, wadanda suka kare daga doron kasa kimanin shekaru miliyan 66 da suka shude.

Rahoton ya kara da cewa, sare dazuka da kuma yawaitar manyan masana’antu, na kan gaba wajen haddasa gurbacewar muhalli, domin a cewar masanan, sare dazukan da ke dada yawaita ne ya haddasa dumamar yanayin da ya haifar da tashin gobarar daji a Australia da Indonesia da Rasha da Portugal da Carlifornia da kuma Girka, wuraren da gobarar ta tafka mummunar barna.