Isa ga babban shafi
Libya

Libya ta haramta kamfanonin Turai a kasar

Kasar Libya ta haramta wa wasu kamfanonin kasashen Turai sama da 40 gudanar da harkokinsu a kasar da suka hada har da kamfanin mai na Total mallakin Faransa.

Firaministan Libya, Fayez-al-Sarraj da shugaban Faransa, Emmanuel Macron a birnin Paris.
Firaministan Libya, Fayez-al-Sarraj da shugaban Faransa, Emmanuel Macron a birnin Paris. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Kudi da kuma Kasuwancin Kasar ta Libya ta fitar a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa kamfanonin na gudanar da harkokinsu na kasuwanci a kasar ne ba a kan ka’ida ba.

Mafi yawan kamfanonin na kasashen Faransa da Jamus da kuma Finland ne, matakin da ke zuwa a daidai lokacin da Firaministan Libya Fayez al-Sarraj ke ziyara a kasashen Turai, yayinda wata majiya ke cewa hakan alama ce da ke tabbatar da cewa Firaministan bai gamsu da sakamakon ganawarsa da shugabannin wadannan kasashe ba.

Sanarwar ta kara da cewa, wadannan kamfanonin sun ci gaba da gudanar da harkokinsu a Libya, duk da cewa yarjeniyoyin da ke tsakaninsu da kasar sun daina aiki tun shekara ta 2010.

A yanzu dai an bai wa wadannan kamfanoni da suka hada da Total na Faransa, Siemens na Jamus da kuma Alcatel wanda reshen kamfanin Nokia na kasar Finland ne, wa’adin watanni uku domin sabunta lasisi matukar dai suna bukatar gudanar da ayyukansu a kasar ta Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.