Isa ga babban shafi
Sri Lanka

An sanya dokar-ta-baci saboda kyamar Musulmai

Gwamnatin Sri Lanka ta sanya dokar-ta-baci a sassan kasar bayan tsanantar zanga-zangar kin jinin mabiya addinin Islama da ta barke a wasu manyan yankuna, matakin da ke da alaka da harin ranar Easter da ya hallaka kusan mutane 300.

Jami'an sojojin Sri Lanka na sintirin tabbatar da tsaro a kasar
Jami'an sojojin Sri Lanka na sintirin tabbatar da tsaro a kasar REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Da ya ke tabbatar da dokar takaita zirga-zirga a sassan kasar ta Sri Lanka, Firaminista Ranil Wickremesinghe ya ce, dokar ta zama wajibi la’akari da yadda zanga-zangar ke neman juyewa zuwa rikicin kabilanci.

A cewar Firaministan, zanga-zangar kin jinin mabiya addinin Islaman marasa rinjaye a kasar, ta fi tsananta a yankunan arewacin kasar, inda wasu kananan kungiyoyi suka rika kona gidaje da makarantu da kamfanoni ko dukiyoyin wadanda basu ji basu gani ba.

Rahotanni sun ce, tsakankanin daga ranar Lahadi zuwa Litinin, kungiyoyin wadanda ba a san ko mabiya wane addini ne ko kabila ba, sun kona tarin shaguna da ababan hawa har ma da masallatai, dukkaninsu mallakin Musulmai, a daidai lokacin da suke tsaka da azumin watan Ramadana.

Cikin jawabin kai tsaye da Firaministan ya gabatar ta gidan Talabijin, ya ce, sai a yammacin yau Talata ne za a janye dokar takaita zirga-zirgar musamman a yankunan kasar 3 da rikicin ya fi tsanta.

Kawo yanzu babu wasu rahotanni da ke nuna adadin mutanen da suka jikkata ko suka rasa rayukansu a farmakin kan mabiya addinin Musulunci, sai dai tuni gwamnatin kasar ta dauki matakin kulle ilahirin dandalin sada zumunta da suka kunshi WhatsApp da  Facebook da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.