rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Diflomasiya Amurka Isra'ila Nukiliya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran: Amurka da Isra'ila za su dandana kudarsu

media
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Amir Hatami. AFP

Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Amir Hatami, ya sha alwashin cewa kasar za ta tilastawa Amurka da Isra’ila fuskantar shan kaye kan manufofinsu na cutar da duniya, musamman matsin lambar da suke mata.


Hatami ya sha alwashin ne yayin da yake jawabi wajen taron tsaffin dakarun tsaron kasar ta Iran a birnin Teheran, a dai dai lokacin da zaman tankiya datayar da jijiyoyin wuya ke dada zafafa tsakanin Iran din da Amurka.

A cewar Ministan tsaron, tun bayan yin juyin juya hali, kasar ta shafe sama da shekaru 40 tana fuskantar barazanar cutarwa daga Amurka, yunkurin da har yanzu bai yi tasiri ba, yanayin da ministan ya sha alwashin shi ne zai ci gaba da tabbata.

Dagantaka ta kara yin tsami tsakanin Amurka da Iran a ‘yan makwannin nan, bayan da shugaba Trump ya fadada takunkuman karya tattalin arzikin da ya kakabawa Iran kan sashin hakar manta zuwa fanninta na hakar ma’adanai, da zummar haramta mata cinikayya da sauran kasashe.

A ranar 8 ga watan Mayu da muke ciki Iran ta bayyana janyewa daga wani bangare na yarjejeniyar Nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya, har sai lokacin da suka samar da hanyoyin dakile tasirin takunkuman da Amurka ta kakaba mata, kan yarjejeniyar nukilyar ta shekarar 2015.