rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Gabas ta Tsakiya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka za ta sake girke dakaru dubu 5 a gabas ta tsakiya

media
Shugaba Donald Trump tare da mai bashi shawara kan harkokin tsaro Lt. Gen. H.R. McMaster REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo

Wasu Rahotanni daga Amurka na nuna cewa ma’aikatar tsaron kasar Pentagon na shirin aikewa da Karin dakarun soji dubu 5 zuwa yankin gabas ta tsakiya dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin Iran da kasashen yankin da ke kawance da Amurkan.


Matakin na Amurka na zuwa dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakaninta da Iran tun bayan daura aniyar dakatar da Tehran daga fitar da albarkatun manta zuwa kasuwannin duniya.

Wasu manyan hafsoshin sojin Amurka da ke shalkwatar tsaron kasar, sun bayyana cewa, cibiyar gudanar da ayyukan soji da kanta ce ta bukaci ma’aikatar da Pentagon da aike da tarin dakarun dubu 5 ga gabas ta tsakiya, sai majiyar ta ce kawo yanzu Pentagon ba ta nuna amincewa da bukatar ba.