rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Jamus

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kamfanin irin shuka na Bayer ya shiga tsaka mai wuya

media
Tambarin Kamfanin Bayer da ke da babbar shalkwata a Jamus REUTERS/Marco Bello

Kamfanin Bayer da ya saye takwaransa na Monsanto mai samar da maganin kwari da kuma ingantaccen iri na shuka, ya sake shiga tsaka mai wuya, dangane da zargin da ake yi wa tsohon kamfanin na leken asirin manyan ‘yan siyasa da wasu jami’ai a nahiyar Turai.


Kalubalen da katafaren kamfanin na Bayer mai hedikwata a kasar Jamus ke fuskanta ya karu ne, bayan da a ranar Talatar da ta gabata ya amince cewar kamfanin Monsanto na hada magungunan kwari da samar da ingantaccen irin shuka da ya saye a 2018, ya aikata laifin yiwa manyan mutane da dama leken asiri a sassan nahiyar Turai.

Mutanen da aka bankado cewar Monsanto kafin Bayer ya saye shi a waccan lokacin ya yiwa leken asiri, sun hada da ‘yan siyasa, ‘yan jaridu da wasu kungiyoyi da alakar aiki ke hada su da kamfanin, wadanda ko dai suna goyon bayan ayyukan kamfanin na Monsanto ko akasin haka, a kasashen Spain, Poland, Jamus, Faransa, Italiya, Holland da kuma Birtaniya.

Tun bayan da Bayer ya saye kamfanin Monsanto kandalabiliyan 63 a shekarar bara, yake fama da kalubalen fuskantar shari’o’I a kotu da suke alaka da lafiya.

Yanzu haka kididdiga ta nuna cewa kamfanin Bayer na fuskantar akalla shara’o’i dubu 13 da 400, wadanda ke zargin kamfanin da haddasa musu kamuwa da cutukan da suka hada da Cancer, sakamakon amfani da magungunan kwari da ya sana’anta ko kuma cin abincin da aka sanyawa magungunan da ya samar.