Isa ga babban shafi
Rasha-Congo

Rasha za ta tallafawa bangaren Sojin Congo brazaville

Rasha za ta aike da kwararru kasar Congo Brazaville don taimaka wa rundunar sojin kasar a fannoni da dama da suka hada da gyara da kuma yadda ake sarrafa wasu manyan makamai kirar kasar ta Rasha.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin Sputnik/Aleksey Nikolskyi/Handout via REUTERS
Talla

Wannan dai na kunshe ne a karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu suka sanya wa hannu a ziyarar da shugaban kasar ta Congo Denis Sassoy Nguesso ya kai a birnin Moscow, inda a jiya ya gana da shugaba Vladimir Putin bayan ya gabatar da jawabi gaban majalisar dokokin kasar.

Rasha wadda ba safai ta fiya shiga harkokin kasashen Afrika ba idan aka kwatanta da takwarorinta na Amurka da Birtaniya Faransa da kuma Jamus, kusan ita ce kan gaba a bangaren harkokin makamai da karfin soji a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.