rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya WHO

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taba na kashe sama da mutane milyan 3 a shekara

media
Hoton taba sigari da aka daukar ranar 8 ga watan oktobar 2014. REUTERS/Christian Hartmann/Illustration REUTERS/Christian Hartmann/Illustration

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da zukar taba sigari, saboda illar da ta ke yi wa bil adama ta fannin lafiya a kowace rana ta Allah.


Bikin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar lafiya ta Duniya ke takun saka da kamfanonin sarrafa tabar sigari, wadanda ke bullo da sabbin dubaru domin janyo hankalin matasa.

Bincike na baya-bayan nan da hukumar lafiya ta duniya ta gudanar, na nuni da cewa akalla mutane milyan 3 da dubu 300 ne ke rasa rayukansu a kowace shekara sakamakon cututuka masu nasaba da zukar taba.

Mafi yawan cututukan na kama huhu ne, yayin da illolin tabar ke shafar hatta yara kanana a cewar masu binciken.