Isa ga babban shafi
Amurka-China

Rikicin kasuwancin China da Amurka ya sake dagulewa

China ta kara yawan harajin da take dorawa kan kayayyakin da Amurka ke shigarwa kasuwanninta.

China ta kara yawan harajin da take dorawa kan kayan da Amurka ke shigarwa kasuwanninta.
China ta kara yawan harajin da take dorawa kan kayan da Amurka ke shigarwa kasuwanninta. REUTERS
Talla

Kayayyakin Amurkan da kasar ta China ta kakabawa harajin kuwa sun kai na dala biliyan 60, wadanda ta karawa harajin kashi 25 cikin 100.

Matakin na China martani ne kan harajin kashi 25, da Amurka ta kara kan kayanta na kimanin dala biliyan 200, lamarin da ya sake dagula rikicin kasuwancin da ya shafe watanni tsakanin kasashen biyu.

A gefe guda kuma Chinan ta ce nan bada dadewa ba, za ta bayyana wasu kamfanoni da ta yanke hulda da su, wadanda ake sa ran na Amurka ne, da kuma wasu na yankin Turai, da suka katse hulda da kamfaninta na kera wayoyin hannu da fasahar sadarwa, wato Huawei a baya bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.