rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Syria Afghanistan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Najeriya na kan gaba wajen fama da rikice-rikice a duniya-Rahoto

media
Rikcin Boko Haram na daya daga cikin manyan kalubalen da ke gaban Najeriya dangane da fafutukar gwamnatin kasar ta ganin ta maido da zaman lafiya a fadin kasar AFP PHOTO/STRINGER

Wani rahoton bincike ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 16 da ke kan gaba wajen fama da tashe-tashen hankula a duniya, abinda ke nuna cewa, Najeriyar ta ci gaba da rike matsayinta na bara.


Rahoton ya nuna cewa har yanzu kasashen Iceland da New Zealand ne ke kan gaba wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, yayinda kasar Portugal ke a matsayi na uku bayan ta kado Austria wadda ta haye matsayi na uku a bara.

Yanzu haka kasar Syria ce ke a matssyi na biyu wajen fama da rikice-rikice, inda aka bayyana Afghanistan a matsayi na farko wajen samun tashe-tashen hankula a duniya.

Rahoton wanda Cibiyar Tattalin Arziki da Kididdigar Zaman Lafiya ta Ukraine ke fitarwa duk shekara, ya ce, kasashen Sudan da Masar da Arewacin Marcedonia da Rwanda sun samu gagarumin ci gaba wajen samun kwanciyar hankali a bana.

Kazalika a wannan karon rahoton ya ce, an samu raguwar mutanen da ke rasa rayukansu a sakamakon rikice-rikice musamman a kasashen Syria da Najeriya.