rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Duniyarmu A Yau

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yawan al'ummar duniya zai haura biliyan 9 a 2050 - MDD

media
Wani yanki na birnin London a watan Disamba na 2018, da ke nuna misalin yadda yawan al'umma zai karu a kasashe masu tasowa da dama, nan da wasu 'yan shekaru. AFP/File

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya y ace yawan mutane a duniya zai karu zuwa biliyan 9 da miliyan 700 nan da shekara ta 2050.


A halin yanzu dai an kiyasta cewa yawan al’ummar duniya ya kai biliyan 7 da doriya.

Rahoton majalisar dinkin duniyar ya kuma yi hasashen cewa idan har ana raye, nan da shekara ta 2100 yawan mutane zai kai biliyan 11 a doron kasa.

Sabon rahoton na cewa kasar China da ake cewa tafi kowace kasa yawa, za ta sami raguwar mutane sosai nan da shekara ta 2050.

Majalisar dinkin duniya ta ce kasashe 9 aka gano za su fuskanci karuwar mutane sosai bisa hasashen da aka yi.

Kasashen kuwa sun hada da India, Najeriya, Pakistan, Jamhuriyar Congo, Habasha, Tanzania, Indonesia, Masar da kuma Amurka.