rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya ‘Yan gudun Hijira

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane miliyan 70 sun tsere daga gidajensu saboda rikici

media
Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallansu saboda rikice-rikice REUTERS/Mohammad Ponir Hossain

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, sama da ‘yan gudun hijira miliyan 70 ne suka tsere daga gidajensu a bara sakamakon tashe-tashen hankula a kasashensu.


A rahotonta na shekara-shakara, Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, an ma takaita adadin mutanen da suka tsere daga gidajen nasu a shekarar 2018 saboda alkaluman da ta bayar basu kunshi daukacin ‘yan gudun hijirar Venezuela ba.

A karshen shekarar 2017 dai, mutane miliyan 68.5 ne aka kidaya cewa, an tilasta musu kaurace wa muhallansu saboda tashe-tashen hankula.

Sai dai a 2018, an samu karuwar ‘yan gudun hijirar saboda rikicin kabilancin da ya addabi kasar Habasha, da kuma matsalar tattalin arziki da ta dabaibaye Venezuela, abinda ya haifar da karancin abinci da magunguna a kasar.

Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, tun daga shekarar 2016, kimanin mutane miliyan 3.3 ne suka tsere daga Venezuela.

A halin yanzu dai, adadin ‘yan gudun hijira a duniya ya ninka a cikin shekaru 20 kuma ya zarce daukacin adadin mutanen kasar Thailand, yayinda kasashen Syria da Colombia ke kan gaba wajen fama da matsalar ta ‘yan gudun hijira.