rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya ta mayar da martani kan kisan Khashoggi

media
Marigayi Jamal Khashoggi MOHAMMED AL-SHAIKH / AFP

Gwamnatin Saudiya ta caccaki rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa, akwai kwararan shaidu game da hannun Yarima Mohamed Bin Salman a kisan Jamal Khashoggi. Rahoton ya kuma bukaci a hukunta masu hannu a kisan dan jaridar wanda aka yi gunduwa-gunduwa da namansa a ofishin jakadancin Saudiya da ke birnin Santanbul a cikin watan Oktoban bara.


Karamin Ministan Harkokin Wajen Saudiya, Adel al-Jubeir ya bayyana cewa, babu wani sabon zance a cikin wannan rahoto na Majalisar Dinkin Duniya domin kuwa rahoton na nanata abubuwan da tuni aka yada wa duniya a can baya ne.

Ministan ya ce, rahoton na dauke da rudani da zarge-zarge marasa tushe, yayinda ya bayyana shakkunsa kan sahihancinsa.

Agnes Callamard, Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya, ita ce ta fitar da rahoton da ke zargin Yariman Mai Jiran Gadon Saudiya da hannu a kisan marigayin dan jaridar.

Callamard ta bukaci Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres da ya kaddamar da binciken kasa da kasa kan kisan.

Tuni dai kasar Turkiya ta ce, ta gamsu da wannan rahoto kuma tana goyon bayan shawarwarin da Callamard ta bayar a rahoton.

Saudiya dai ta wanke Yariman dangane da zargin da ake yi masa, yayinda ta tuhumi mutane 11 da ake zargi da hannu a kisan da suka hada da mutane biyar da ake ganin za su fuskanci hukuncin kisa.