Isa ga babban shafi

Gidan sarautar Saudiyya na da hannu a kisan Khashoggi - Rahoto

Mai binciken musamman ta Majalisar Dinkin Duniya Agnes Callamard, ta gabatar da rahoton binciken da ta yi game da kisan gillar da aka wa dan jaridar nan na kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi a gaban hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar.

Yerima Mohamed Ben Salman (MBS)
Yerima Mohamed Ben Salman (MBS) Bandar Algaloud/REUTERS
Talla

A ranar Laraba, da misalin karfe daya agogon GMT Callamard ta gabatar da rahotonta a gaban Hukumar Kare Hakin bil Adama a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A rahoton mai shafi dari, wadda ya fito a ranar 19 ga wata Yuni, Callamard ta ce, kisan Khashoggi a ofishin jakadancin Saudiyya dake Istambul a watan Oktoban shekarar da ta gabata wani abu ne da aka kitsa, kuma gidan sarautar Saudiyyar na da hannu dumu dumu a aika – aikar.

Rahoton ya kuma bada shawarar cewa a binciki Yeriman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman, mai inkiya da MBS game da kisan dan jaridar.

Saudi Arabiya mamba ce a Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma ba mamaki, wakilanta na zaune a zauren taron yayin da Callamard ke gabatar da rahotonta.

Rahoton yayi nuni da yadda Saudiyya ta take yarjejeniyar huldar diflomasiyya da aka cimma a Vienna, da kuma dokar Majalisar Dinkin Duniya da ta yi hani da amfani da karfi yayin da ake zaune kalau, tare da wacce ta bada damar rayuwa ba tare da dakilewa ba.

Firaministar Birtaniya mai barin gado, Theresa May, tayi kira da a bi diddigin wannan kisan gillar har sai gaskiya ta yi halin ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.