Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na shan suka kan mutuwar bakin haure

Hoton gawar wani mutum dan kasar El-Salvado da 'yarsa mai shekaru biyu da suka mutu a teku a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa Amurka, ya haifar da mummunar suka kan matakan da shugaba Donald Trump ke dauka kan baki.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP
Talla

Beto O’Rouke, tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Texas da ke neman ganin Jam’iyyar Democrat ta tsayar da shi takara a zaben shekara mai zuwa, ya bayyana karara cewar shugaba Trump ke da alhakin mutuwar mutanen biyu.

Sanata Camala Harris daga California ya ce, wadannan baki da ke tserewa daga kasashensu na fuskantar tashin hankali ne wanda ya kamata a basu mafaka, amma da zaran sun iso sai Trump ya ce musu su koma gida, abinda ke kai ga mutuwarsu.

Rashida Tlab, 'yar Majalisar Wakilai daga Michigan da ta bukaci tsige shugaba Trump ta dora wa abinda ta kira gwamnati mara imani alhakin mutuwar mutanen.

Shi kuwa Sanata Chuck Schumer daga New York ya gabatar da hotan mamatan ne a zauren Majalisa, inda yake cewa tayaya shugaban kasa zai ga wannan amma ya kasa fahimtar cewar wadannan mutane na tserewa tashin hankali ne.

Shi ma Fafaroma Francis ya bayyana takaicinsa da mutuwar, inda ya yi addu’a ga mamatan da kuma daukacin 'yan gudun hijirar da ke tserewa inda ake samun tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.