rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Amurka Iran Nukiliya Emmanuel Macron Donald Trump Hassan Rouhani

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ba ma fatan yakar Iran sai idan ta tirsasa- Trump

media
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake jaddada matsayin sa na cewar baya bukatar gwabza yaki da kasar Iran, amma idan hakan ya zama dole, yakin ba zai dade ba.


Trump ya kuma bayyana cewar ba zai tura koda soja guda kasar Iran ba, yakin da zai gudana za’a fafata shi ne ta kai hare haren sama.

Kalaman shugaban na zuwa ne jim kadan bayan tattaunawar da akayi tsakanin shugaba Hassan Rouhani da Emmanuel Macron, inda shugaban na Iran ya ce baya bukatar yaki da Amurka.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa dai na neman ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen warware rikici tsakanin kasashen biyu ne, musamman bayan tsanantarsa a baya-bayan nan.

Tsamin alaka ya kara tsananta tsakanin Amurka da Iran ne bayan da Tehran ta kakkabo wani jirgin Washington marar matuki da ya shigo iyakarta, matakin da ya kai ga kakaba mata sabbin takunkuman karya tattalin arziki.