rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Za mu gayyaci mai girma Kim zuwa Washington- Trump

media
Shugaba Donald Trump a ganawarsa da takwaransa na Korea ta Arewa Kim Jong Un Brendan Smialowski / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya amsa tambayar cewa nan gaba kadan zai gayyaci shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un zuwa birnin Washington DC fadar gwamnatin kasar don tattaunawa da shi, a wani mataki na sake nunawa duniya karfin alakar da ke tsakanin kasashen biyu masu adawa da juna a baya.


Donald Trump wanda ke amsa wata tambaya daga manema labarai bayan kammala ganawar su da Kim yau Lahadi a kan iyakar Korea ta Arewan da makociyarta Korea ta kudu, ya ce tabbas ya na da shirin gayyatar Kim Amurka.

A cewar Donald Trump gayyatar Kim zuwa Amurkan zai kara karfin alakar da a yanzu haka ke tsakaninsu.

Bayan kammala taron G20 a birnin Osaka na Japan ne kai tsaye Donald Trump ya wuce Korea ta kudu, inda ya gayyaci Kim Jong Un na Korea ta arewa don gaisawa a kan iyakar kasashen biyu.

Cikin Kalaman Trump gaban Manema labarai ya ce bai tsammaci amsa gayyatar daga mai girma Kim Jong Un ba, cikin fara'a dai shugabannin biyu suka kammala tattaunawar, ko da dai dama Donald Trump ya ce ganawa ce kawai ta gaisawa da juna a matsayinsu na abokai.

Alaka tsakanin kasashen Amurkan da Korea ta Arewa na ci gaba da gyaruwa ne dai tun bayan ganawar shugabannin biyu har sau 3 a shekarun bara da bana, wanda ke neman kawo karshen kiyayyar tsawon shekaru tsakanin bangarorin biyu.

Ko bayan ganawa tsakanin Kim da Trump a Vietnam sai da Korea ta arewan ta sake wani gwajin makamai mai linzami amma kai tsaye Amurka ta bayyana cewa bai saba ka'ida ba.