rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Iran Nukiliya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron ya damu kan yadda Iran ta fara karya ka'idojin yarjejeniyar 2015

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron Ian Langsdon/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanule Macron ya bukaci kasar Iran da ta gaggauta rage adadin sinadarin uranium da ta ke tacewa yanzu haka, bayan da hukumar yaki da yaduwar makamin nukiliya ta IAEA da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif suka tabbatar da cewar kasar ta zarce adadin da aka gindaya mata a karkashin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015.


Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana damuwar sa kan yadda Iran ta zarce ka’idar da aka shata mata na ta ce sinadarin uranium a karkashin yarjejeniyar ta shekarar 2015 da ta kulla da kasashen duniya, inda ya bukace ta da ta gaggauta dakatar da shirin da kuma daukar duk wani mataki da kan iya yi wa yarjejeniyar zagon kasa.

Macron ya ce zai cigaba da daukar matakin warware matsalolin da ake samu tsakanin Iran da Amurka wanda zai bai wa kasar damar cin gajiyar yarjejeniyar da aka kulla, mussaman wadanda suka shafi tattalin arzikin ta.

Ita ma kasar Rasha ta hannun Ministan harkokin wajen ta, Sergei Lavrov, ta bukaci Iran da ka da ta yi amfani da bacin rai wajen daukar matakan da ba su dace ba.

Ita ma China ta bayyana damuwa kan sabawa yarjejeniyar, inda ta zargi Amurka da haifar da matsalar.