wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Yan wasan Amurka mata sun koma gida cike da murna

Duban magoya bayan kungiyar kwallon kafar Amurka ta mata ne suka halara a birnin NewYork wajen tarben yan wasan bayan gaggarumar nasara da suka samu tareda lashen kofin Duniya na kwallon kafa da ta gudana a lyon dake kasar Faransa tareda doke Netherlands da ci 2 da nema.
An dai bayyana cewa yan kasar na sayen rigunan yan wasa dake dauke da alamomin tarmamu hudu dake da nasaba da nasarori hudu da suka samu tareda lashe kofin Duniya sau hudu.
Wasu daga cikin yan wasan yanzu haka sun bayyana cewa ba za su amsa goron gayata daga fadar Shugaban kasar ba.