rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Boeing ya bayyana shirin barin aikin

media
Jiragen kamfanin Boeing REUTERS/Mike Blake

Shugaban Kamfanin kera jiragen Boeing, bangaren dake kula da MAX 737 da aka dakatar da aiki da shi a Duniya saboda haduran da aka samu, Eric Lindblad ya bayyana aniyar sa na aje aikin sa, a daidai lokacin da kamfanin ke cigaba da fuskantar matsaloli.


Shugaban kamfanin Kevin McAllister ya bayyana shirin barin aikin Lindblad, a wannan lokaci da kamfanin ke kokarin shawo kan masu tabbatar da ingancin jiragen sama sun amince da sauye sauyen da kamfanin yayi kan samfurin jirgin da ya hallaka mutane 346 a hadura guda biyu.

McAllister ya bayyana cewar wannan mawuyacin lokacin ne a gare su, a daidai lokacin da suka mayar da hankali wajen dawo da ingancin jiragen kamfanin samfurin MAX 737.