rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Mexico

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Samamen cafke 'yan ci-rani a cikin kasar Amurka

media
Donald Trump Shugaban Amurka Brendan Smialowski / AFP

Yau lahadi jami’an tsaron Amurka za su kaddamar da samame a kan baki da ke zaune kasar ba a kan ka’ida ba tare da tasa keyarsu zuwa kasashensu kamar dai yadda shugaba Donald Trump ya bayar da umurni.


A matakin farko na wannan samame, jami’an shige-shige da fice na kasar sun yi hasashen kama akalla mutane dubu biyu da ke zaune cikin mayan biranen 10.

Za a kaddamar da samamen ne a kan mutanen da tuni aka tantance wuraren da suke zaune a cikin kasar ta Amurka, duk da cewa wasu daga cikinsu sun jima zaune a kasar amma ba tare da sun mallaki takardu ba, yayin da wasu ma ke tare da iyalansu.