rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Turkiya Rasha Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Na'urar kakkabo makamai da Rasha ta kerawa Turkiya sun isa hannunta

media
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan Reuters/路透社

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana farin cikin sa da samun na’urorin kakkabo makamai masu linzami daga Rasha, duk da adawar da Amurka keyi da cinikin.


Yayin da ya ke jawabi a ranar da kasar ta cika shekaru 3 da yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba, Erdogan ya ce sun fara karbar wadannan makamai wadanda wasu ke cewa ba za su iya ba.

A watan Yulin shekarar 2016 wasu sojin kasar suka yi yunkurin kifar da gwamnatin Erdogan, abinda ya yi sanadiyar kashe akalla mutane 250, yayin da sama da 2,000 suka samu raunuka.

Kawo yanzu dai Gwamnatin Turkiya na ci gaba da kame tare da hukunta daidaikun mutanen da ke hannu ko kuma masaniya koma suka taimakawa yunkurin juyin mulkin.

Kasar Amurka dai tun bayan fara cinikin makaman tsakanin Rasha da Turkiyan ta gargadi Erdogan kan cinikin wanda ta ce barazana ne ga tsaro, baya ga yi masa barazanar karin takunkumai da kuma koro daliban Turkiyan da ke karatu can a Amurka.