rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

WHO Lafiya Ebola Majalisar Dinkin Duniya Jamhuriyar Demokradiyyar Congo Duniyarmu A Yau

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yaduwar Ebola a Congo barazana ce ga duniya - WHO

media
Wasu daga cikin al'ummar birnin Goma, yayin karbar rigakafin kamuwa da cutar Ebola. REUTERS/Olivia Acland

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yaduwar cutar ebola a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo a matsayin abin damuwa ga kasashen duniya.


Shugaban hukumar Tedros Adhanom Gebreyesus yace lokaci yayi da za’a fadakar da duniya barazanar da cutar ke dauke da shi, kamar yadda kwamitin kwararru ya bada shawara akai.

Gebreyesus yace duk da yake daukar matakin ba zai sauya assalin abinda ke faruwa a Congo ba, amma kuma zai bada damar sanar da duniya domin ganin an dauki matakan da suka dace na shawo kan cutar.

Wannan shine karo na farko da Hukumar ta dauki irin wannan mataki bayan irin wanda aka yiwa cutar murar tsintsaye a shekarar 2009 da polio a shekarar 2014 da ebola a shekarar 2014 zuwa 2016 da kuma Zika a shekarar 2016.