Isa ga babban shafi
Rasha

Zanga-zangar yan Adawa a Rasha

A Rasha sama da mutane dubu 10.000 ne suka fito a wata zanga-zanga da ta gudana tsakiyar birnin Moscow inda suka bukaci ganin an gudanar da zaben kananan hukumomi masu inganci da kuma suka bi tafarkin Demokkuradiya a wannan kasa.

Zanga-zangar yan adawa a kasar Rasha
Zanga-zangar yan adawa a kasar Rasha REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Gangamin na yau daga yan adawa na zuwa ne biyo bayan soke takarar da dama daga cikin yan takara da suka shigar da takardar su na neman kujerar Shugabancin da’irar birnin Moscow, zaben da za a yi a watan Satumbar shekarar bana.

Gwamnatin kasar ta aike da jami’an tsaro da za su bayar da kulawa domin kaucewa duk wani rikici ko tashin hankalin da kan iya biyo bayan wannan zanga-zanga.

Yan adawa ta bakin Alexeï Navalny ya bayyana cewa kusan mutane dubu 20 ne suka fito,wanda hakan ne karo na farko da aka samun yawan jama’a a zanga-zangar kasar Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.