rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ukraine

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyar Shugaban Ukraine ta lashe zaben yan Majalisa

media
Zelensky Shugaban kasar Ukraine GENYA SAVILOV / AFP

A kasar Ukraine, an gudanar da zaben yan majalisu, alkaluman farko na bayyana jam’iyar Shugaban kasar Volodomyr Zelensky da cewa ta samu gaggarumar nasara da yawan yan Majalisu.


A zaben Shugaban kasar da ya gudana a watan Afrilu Volodymyr Zelensky ne ya lashen zaben a gaban abokin hamayar sa,tsohon Shugaban kasar Petro Poroshenko,wanda nan take ya kira Zelensky na jam’iyyar adawa kuma fitaccen dan wasan barkwancin da suka yi takara tare, ya kuma taya shi murnar nasarar lashe zaben.

Sakamakon farko da ake da su yanzu haka na nuni cewa Jam’iyar Shugaba Volodomyr ta samu kashi 43 cikin dari na kuri’u da aka kada.

A jawabin sa na farko yan lokuta da kawo karshen zaben,Shugaban kasar ya dau alkawali na aiwatar da sauye-sauye ta sukar tattalin arziki a Ukraine.