rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Faransa Emmanuel Macron Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Baraka ta sake kunno kai tsakanin Trump da Macron

media
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump US President Donald Trump (R) is welcomed by French president Em

Sabuwar takaddama ta sake kunno kai tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. Shugaban na Amurka ya danganta Shugaban Faransa a matsayin mutumen dake da raunin.


Donald Trump Shugaban Amurka a yau juma’a ya danganta Shugaban Faransa da kidimamme,tare da yin barazanar kara haraji kan wasu haajoji da Faransa ke shigarwa Amurka musaman wata nau'in barasa 'yar Faransa.

Matakin na Donald Trump dai na zuwa ne biyo bayan harajin da Faransa ta sanar da kakabawa kan wasu daga cikin manyan kamfanonin Sadarwar Amurka.

Kamar da yada Shugaban na Amurka ya saba,ya aike da sakon na sa ne ta hanyar Twitter, inda ya bayyana cewa idan akwai wata kasa da za ta iya kakaba makamancin harajin to Amurka ce amma ba Faransa ba.

Cikin sakon na Twitter Donald Trump ya ce Macron ya jira martaninsa nan gaba kadan, don kuwa zai mayar da martani kan shirmen da Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya aikata.

Donald Trump ya kuma bayyana cewa, ya sha nanata cewa har kullum nau'in barasar Amurka ta zarce ta Faransa a kima da kuma dandano.