Fursunoni 52 sun mutu a rikicin gidan yarin Brazil
Akalla fursunoni 52 sun rasa rayukansu sakamakon kazamin fadan da ya kaure tsakanin wasu kugiyoyin 'yan daba da basa-ga-maciji da juna a gidan yarin da ake tsare da su a kasar Brazil.
Wallafawa ranar:
Wannan ne rikici na baya–bayan nan da ya addabi wannan gidan yarin mai matsanancin cinkoso da hatsari a jihar Para.
Wani jami’in Hukumar Kula da Gidan Yarin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, daga cikin fursunonin da aka kashe har da guda 16 da aka fille musu kawuna a tarzomar ta tsawon sa'a guda.
Ko a watan Mayun da ya gabata, sai da aka kashe akalla fursunoni 55 a gidajen yari daban-daban a jihar Amazonas mai makwaftaka da jihar Para sakamakon rikice-rikecen 'yan daban.
Brazil ce kasa ta uku wajen yawan fursunoni da ke garkame a gidajen yari a duniya bayan Amurka da China.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu