rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Amurka Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta soki Amurka kan harajin barasa

media
Donald Trump Shugaban Amurka REUTERS/Jonathan Ernst

Ministan Ayyukan Noma na kasar Faransa, ya yi kakkausar suka ga barazanar da shugaba Donald Trump ya yi, inda yake cewa zai kara haraji kan barasar da ake sarrafawa a Faransa don shigar da ita a Amurka.


Donald Trump ya yi wannan barazanar ce a matsayin martani dangane da harajin da Faransa ta dora wa kamfanonin kere-keren kimiya mallakin Amurka.

Ministan noman na Faransa Didier Guillaume ya ce, duk wani matakin lafta sabon haraji a kan barasar da kasar ke shigarwa Amurka zai kasance wauta, saboda Trump na barazanar kara harajin ne ba don komai ba sai domin kawai Faransa ta amince da sabuwar dokar haraji kan kamfanonin kere-kere da ake kira Gafa.

Ministan na Faransa ya ce, karin haraji a kan kamfanonin kere-keren ba wani laifi a cikinsa idan aka yi la’akari da ribar da suke ci, kuma babu inda hakan ya saba wa doka.

Ranar Juma’ar da ta gabata ne Trump ya yi dirar mikiya a kan takwaransa na Faransa Emmanuel Macron bayan amincewa da dokar haraji kan kamfanonin kere-keren kimiyar, inda a nasa bangare Trump ya ce, zai dauki fansa ta hanyar dora sabon haraji kan barasar da ake sarrafawa a Faransan.