Isa ga babban shafi
Amurka

'Yan takarar Democrat sun tafka muhawara kan baki

Manyan 'yan siyasar da ke neman Jam’iyyar Democrat ta tsayar da su takarar shugabancin Amurka sun sake fafatawa a tsakaninsu a mahawara ta biyu da ta gudana a Detroit, inda Bernie Sanders da Elizabeth Warren suka kare manufofinsu na kiwon lafiya da kuma karbar baki.

'Yan takarar Democrat da suka fafata da juna
'Yan takarar Democrat da suka fafata da juna REUTERS/Rebecca Cook
Talla

Warren ta bayyana bukatar sake fasalin inshorar lafiya wadda shugaba Donald Trump ya sauya domin taimakawa masu hannu da shuni, yayinda John Delaney ya caccaki manufofin Sanders da Warren wanda ya bayyana a matsayin abinda zai karya tattalin arzikin kasar.

Delaney ya ce 'yan takarar biyu na gabatar da manufofi marasa inganci da suka shafi kual da lafiyar jama’a da komai kyauta wadanda manufofi ne masu wahala da za su karkata zuciyar masu zabe wajen goyan bayan shugaba Donald Trump.

A yau Laraba ake saran wasu karin 'yan Democrat 10 da suka hada da Joe Biden da Kamala Haris za su tafka tasu muhawarar wadda za a watsa kai tsaye ta gidajen talabijin.

A watan Yulin badi ne jam'iyyar Democrat za ta sanar da wanda ya cancaci tsaya mata takara a zaben wanda za a gudanar a cikin watan Nuwamban shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.