rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Hakkin Mata Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya ta soke dokar tilastawa mata yin tafiya tare da muharrami

media
Wasu dalibai mata a birnin Riyadh na Saudiya. 2/10/2018. REUTERS/Faisal Al Nasser/File Photo

A ci gaba da sauye-sauyen da Saudi Arabia ke aiwatarwa, gwamnatin kasar ta kawo karshen dokar dake tilastawa mata tafiya kasashen waje tare da rakiyar wani muharramin su namiji.


Matakin na zuwa ne bayan kwashe dogon lokaci masu fafutukar neman ‘yanci na adawa da ita, yayin da aka rawaito wasu matan kasar na tserewa daga sa idon ‘yan rakiyar su a kasashen waje.

Sabuwar dokar da aka wallafa tace za’a dinga baiwa duk wani dan kasa fasfo ba tare da an bukaci mata su gabatar da sunayen muharraman su ba.

Sabon sauyin ya baiwa mata a Saudiya ‘yanci gudanar da al’amuransu da dama ba tare da sa’ido ba, matakin da masu fafutukar nemawa matan ‘yanci suka bayyana a matsayin gagarumin ci gaba.

Sabuwar dokar ta kuma baiwa matan Saudiya ‘yancin yiwa ‘ya’ya rijistar haihuwa, yin rijistar aure da rabuwa, sai kuma damar zama mai kula ko wakilan yara kanana, ayyukan da a baya suka rataya a wuyan maza kawai.