rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan bindiga ya kashe masu siyayya 20 a jihar Texas ta Amurka

media
Wasu tarin jami'an tsaro da aka aike yankin na El Paso a jihar Texas yayin faruwar harin a jiya Asabar Joel Angel JUAREZ / AFP

Akalla mutane 20 aka tabbatar da mutuwarsu bayan harin dan bindigan da ya bude wuta kan masu siyayya a wani shagon zamani da ke yankin El Paso na jihar Texas a Amurka. Harin wanda ya faru a jiya Asabar tuni aka fara alakanta shi da na nuna kyama.


Tuni dai Jami'an 'yan sanda suka kame mutumin da ya kaddamar da harin yayinda suka ce za a fara yi masa tuhuma.

Harin wanda shi ne na baya-bayan nan da aka kaddamar a kasar ta Amurka mai fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga wanda ke da nasaba da nuna wariya ko kuma kyama ya kuma jikkata mutane 26.

Tuni dai shugaban kasar ta Amurka Donald Trump da gwamnan jihar ta Texas suka yi tir da harin yayinda jami’an tsaro suka ce suna ci gaba da gudanar da bincike bayan kame maharin.

Harin dai shi ne irinsa na biyu cikin mako guda a irin shagunan zamanin, haka zalika ya zo ne bai wuce kwanaki 7 dafaruwar makamancinsa a jihar California ba.