rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Amurka Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Birtaniya da Amurka za su hada karfi wajen tsaron tekun Fasha

media
Wani jirgin sojin Amurka da ke bayar da tsaro ga tankar dakon mai a mashigin ruwan Hormouz © REUTERS/Hamad I Mohammed

Birtaniya ta bayyana aniyarta ta hada karfi da Amurka wajen aikin kare tankunan man da ke zirga zirga a tekun Fasha, a daidai lokacin da zaman tankiya ke ci gaba da zafafa tsakanin Iran da Amurka, matakin da ke zuwa bayan gorin da Iran ta wa Amurkan kan cewa mukarrabanta na dari-darin bata goyon baya kan kudirin ta.


Shawarar Birtaniya ta shiga rundunar sintirin teku ta musamman karkashin jagorancin Amurka ta yi hannun riga da ainihin manufofinta, bayan kokarin yin haka da kasashen Turai, a zamanin shugabancin Theresa May ya ci tura.

Sai dai a wannan karon amincewar ya biyo bayan matakin kwace jiragen ruwa da Iran ke yi ciki har da Birtaniyar 2, wanda ke cikin jerin jirage 3 da Iran ta kwace cikin kasa da wata guda.

A wata sanarwa, Sakataren tsaron Birtaniya Ben Wallace ya ce kasarsa ta kudiri aniyar tabbatar da cewa jiragen ruwanta ba sa fuskantar barazana, saboda haka ta shiga wannan sabon shirin tsaron teku a yankin na Fasha.

Wannan sanarwar da ta fito daga ma’aikatar tsaron ta Birtaniya ba ta yi wani karin bayani kan ko kasashe nawa ne, idan ma akwai, za su shiga wannan sabon shirin ba.

Kallon hadarin kaji tsakanin Amurka da Iran na ci gaba da kamari ne, tun bayan da shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliya 2015, sannan ya rika antaya wa Iran din takunkuman karayar tattalin arziki, lamarin da ke sanya fargaba a yankin tekun Fasha.