Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta soki shirin Amurka da Turkiya na kafa yankin tsaro a kasar

Gwamnatin Syria ta yi watsi da matakin Amurka da Turkiya na kafa wani yankin tsaro a arewacin kasar da zai haramtawa kowanne bangare kai farmaki yankin, matakin da tuni kungiyar Kurdawan kasar ta yi maraba da shi.

Shugaba Bashar al Assad na Syria
Shugaba Bashar al Assad na Syria SANA / AFP
Talla

Tun a jiya Laraba ne, kasashen na Amurka da Turkiya suka cimma matsaya game da samar da yankin na Tsaro a arewacin kasar ta Syria wanda ke da nufin tabbatar da yankin a matsayin tudun mun tsira tare da haramta kai farmaki kansa, musamman don kawo karshen rikicin da ke tsakanin Turkiyan da Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka.

Kawo yanzu dai babu bayanai game da fadi ko kuma girman yankin da zai zamo na tsaron a arewacin kasar ta Syria karkashin jagorancin Amurkan da Turkiya ko da dai tuni matakin ya ci karo da kakkausar suka daga gwamnatin shugaba Bashar al-Assad wanda Sojinsa ke ci gaba da kokarin kwace yankunan kasar daga hannun ikon mayakan jihadi da ‘yan tawaye.

Shirin samar da yankin tsraon na da nufin bayar da cikakkiyar kariya ga mayakan kurdawa wadanda ke fuskantar barazanar hare-hare daga Turkiya wadda ke kallonsu a mastayin ‘yan ta’adda.

Cikin sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Syria ta fitar a yau Alhamis ta yi kakkausar suka ga matakin tare da yin watsi da yarjejeniyar, inda abnagare guda ta bukaci mayakan Kurdawa su kaucewa mara baya ga matakin wanda ta bayyana a wani yunkurin mamaye kasar ta Syria daga Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.