rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Yemen Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

MDD za ta fara rarraba kayan abinci a Yemen

media
Wani dan Yemen dauke da abincin agaji daga Majalisar Dinkin Duniya. MOHAMMED HUWAIS / AFP

Majalisar Dinkin Duniya za ta maido da shirinta na rarraba kayayyakin abinci a yankunan da ke karkashin ikon yan’ tawayen Huthi a Yemen, inda za ta soma da babban birnin kasar Sanaa a mako mai zuwa.


Kimanin watanni biyu kenan da Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da shirin rarraba kayayyakin abincin bayan zarge-zargen da aka samu kan karkata akalal  abincin na fararen hula.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, 'yan tawayen Huthi sun bada tabbacin cewa, a wannan karo, abincin zai isa ga fararen hula domin cin gajiyar shirin.

Mai magana da yawun shirin, Herve Verhoosel a birnin Geneva, ya ce za’a soma rarraba kayayyakin abincin ga mutane dubu 850 a birnin Sanaa, abinda zai ba su damar gudanar da bukukuwan sallar layya cikin wadata da walwala.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana  Yemen a mastayin kasar da ta kowacce kasa bukatar agaji, inda mutane miliyan 24.1 ke cikin matsananciyar bukatar taimako.

Rikici tsakanin 'yan tawayen Huthi da ke samun goyon bayan Iran da kuma dakarun gwamnati da ke samun goyon bayan rundunar kawance da Saudiya ke jagoranta,  ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla dubu 10.