rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kimanin mahajjata miliyan 2 na hawan Arfa a Saudiyya

media
Dutsen Arfa mai nisan kilomita 15 daga birnin Makkah. AHMAD MASOOD/REUTERS

Yau asabar 9 ga watan Zul Hijja shekara ta 1440 bayan hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Birnin Madina, al’ummar Musulmi dake halartar aikin hajjin bana ke hawan Arfa, daya daga cikin ginshikan ibadar dake cikin jerin shika shikan Addinin Musulunci, yayinda a sassan duniya ragowar al’ummar Muslumin ke azumtar wannan rana.


Dutsen Arfa shi ne wurin da Annabi Muhammad Sallahu Alaihi Wa Sallam ya gudanar da hudubarsa ta karshe ga al’ummar Musulmi kafin Wafatinsa.

Kimanin Musulmi miliyan biyu ne ke gudanar da aikin Hajjin bana, taron addinin Musulunci mafi girma, wanda aka soma daga ranar Juma’a.

Ana bukatar dukkan Musulmin da ya samu dama da kuma wadata, ya gudanar da aikin Hajji akalla sau daya a rayuwarsa.

Bayan gudanar da hawan Arfa, al’ummar Musulmi a fadin duniya ke gudanar da bukukuwan sallar layya da aka fi sani da salla Babba a kasar Hausa.

Kamafanin dillancin labaran Saudiya, ya rawaito cewar, mahajjatan bana sun gudanar da zaman Mina, a tantin da ka iya daukar mutane akalla miliyan 2 da dubu 600.