rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

China Amurka Taiwan

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

China ta tayar da jijiyar wuya kan shirin Amurka a Taiwan

media
Tutocin da kudaden kasasahen China da Amurka REUTERS/Jason Lee/Illustration/File Photo

China ta yi kakkausar suka a game da shirin da Amurka ke yi don aika wani jirgin ruwa makare da makamai zuwa Taiwan, yankin da China ke kallo a matsayin mallakinta.


Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta sanar da cewa kasar ta amince da sayar wa Taiwan jiragen yaki na zamani samfurin F-16 har guda 66 akan kudi Dala bilyan 8, matakin da ke zuwa watanni kadan bayan da Amurkan ta sayar wa yankin da wasu tarin makamai.

Wannan dai daya ne daga ciniki jerin kwangilolin kere-keren makamai da aka kulla tsakanin Washington da kuma yankin na Taiwan da China ke ci gaba da ikirarin cewa mallakinta ne.

A martanin da ya fitar a wannan Laraba, kakakin gwamnatin China Geng Shuang ya ce kasar za ta dauki matakai ciki har da takunkumai a kan kamfanonin Amurka da ke da hannu wajen sayar wa Taiwan wadannan makamai.

China ta bayyana cinikin a matsayin shisshigi da Amurka ke yi a lamurran da suka shafi cikin gidanta, to sai dai a wata sanarwa da ya fitar, Sakataren Wajen Amurka Mike Pompeo ya ce, ba zancen ja da baya a game da wannan ciniki, domin kuwa tuni shugaba Donald Trump ya sanar da majalisa rubuce.