rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya Lebanon Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

"Dole a kai zuciya nesa tsakanin Isra'ila da Lebanon"

media
Wasu daga cikin dakarun Hezbollah na Lebanon Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin da ke tayar da jijiyoyin wuya da su kai zuciya nesa bayan rahotannin da ke cewa, Isra’ila ta yi amfani da jirgi mara matuki wajen kaddamar da farmaki kan maboyar dakarun Hezbollah a yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon.


Mai magana da yawun Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric ya ce, kawo yanzu Majalisar ba ta tabbatar da rahotannin hare-haren da aka kai a ranar Lahadin da ta gabata ba, wadanda su ne na baya-bayan nan da aka gani a ‘yan kwanakin nan a yankin Hezbollah.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin biyu da su kauce wa daukar mataki na zahiri ko kuma musayar kalamai, tana mai cewa dole ne kowanne bangare ya mutunta ka’idojin da Kwamitin Sulhu na Majalisar ya gindaya.

Majalisar ta ce, tana da masaniya kan kalaman shugaban Lebanon, Michel Aoun, wanda ya caccaki farmakin na jirgin mara matuki, tare da bayyana shi a matsayin shealar yaki.

Dakarun Hezbollah da rundunar sojin Lebanon sun nuna wa Isra’ila yatsa game da wannan harin duk da cewa, kasar ta Isra’ila ba ta ce uffam ba kawo yanzu.