Isa ga babban shafi

Dumamar yanayi na barazana ga amfanin tekuna- Rahoto

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan illar dumamar yanayi, ya bayyana yadda tekunan da ke taimakawa wajen wanzuwar dan adama da ci gabansa a ban kasa ke neman juyewa zuwa hanyar cutuwar dan adam sanadiyyar dumamar yanayi wadda yanzu haka ke ci gaba da banna a sassa daban-daban na duniya.

Tsaunukan kankara da ke cikin tekuna
Tsaunukan kankara da ke cikin tekuna Kate RAMSAYER / NASA / AFP
Talla

Rahoton wanda kwamitin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar a yau Alhamis ya nuna cewa sauye-sauyen da aka samu da gurbatattun sinadaran da ke yawo a ban kasa na matukar tasiri wajen lalata tekuna da dazuka wadanda ke taimakawa wanzuwar dan adama a ban kasa.

Rahoton mai dauke da shafi dari 9, shi ne irinsa na 4 cikin kasa da shekara guda da Majalisar ta fitar wanda ke gargadi kan yadda dumamar yanayin ta yi gagarumar illa ga halittun ruwa ta na mai cewa nan gaba kadan za ta kai matakin da za a gaza magance matsalar da ta ke haifarwa.

Rahoton ya nuna yadda habakar tsaunukan kankarar teku na Glaciers ke matukar raguwa yayinda wadda ake da ita ke ci gaba da narkewa cikin wannan karni, matakin da ke hallaka halittun da suka dogara da ita wajen rayuwa.

Ka zalika rahoton ya gwada misali da kanfar kifayen teku wadanda dumamar yanayin ke hallakawa baya ga ambaliyar ruwa wanda rahoton ke bayyana cewa yawaitar ambaliyar da duniya ke fuskanta na da nasaba da karancin wasu halittu a cikin tekunan wanda kuma kai tsaye rashin daukar matakai kan dumamar yanayin ce ke haifarwa.

Bugu da kari rahoton ya gwada misali da matsalar tsananin zafin da yankunan masu matukar sanyi suka fuskanta a bana wanda ya bayyana cewa shima guda ne cikin kalubalen da sauyin ko kuma dumamar yanayin ke haifarwa a ban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.