rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Gasar Zakarun Turai Faransa Spain

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Neymar ya koma Barcelona

media
An kammala cinikin Neymar zuwa Barcelona REUTERS/Mike Segar

Bayan da aka kwashe tsawon lokaci ana dakon ganin ko ina zai koma, shahararren dan wasan kasar Brazil Neymar Junior, daga karshe dai ancimma matsaya tsakanin kungiyar PSG ta kasar Faransa da Barcelona ta Spain, domin ya koma tsohuwar kungiyarsa dake Camp Nou.


Wannan matakin dai ya tabbatar da burin Neymar mai shekaru 27, na yiwa tsohuwar kungiyarsa Barcelona kome, a dai-dai lokacin da ake daf da rufe hada-hadar cikinkin ‘yan wasa a farkon watan Satumba.

An cimma wannan matsayar ce, bayan da Barcelona ta ware zunzurutun kudi Euro miliyan 200, tare da Karin ‘yan wasa uku, wato mai tsaron bayanta Jean-Clair Todibo, da na tsakiya Ivan Rakitic sai kuma Ousman Dembele a matsayin aro har tsawon kaka daya.

Idan mukayi tuni, Neymar ya koma PSG ne a shekarar 2017, bayan da aka sayeshi kan Euro miliyan 222, a matsayin dan wasa da yafi tsada a duniyar tamola.

Tuni mai horas da ‘yan wasan PSG Thomas Tuchel, ya shaidawa manema labarai cewar Neymar bazai buga wasan Ligue 1 da kungiyar zata kara da Metz ba yau Jumma'a.

Yayin da ake saran dan wasan ya yi fafatawarsa ta farko a Club din dake Camp Nou, kafin ranar Litinin a wasannin La Liga.

A tsawon shekaru 2 da ya yi a gasar Ligue 1 na kasar Faransa, duk da yasha fama da rauni, Neymar ya ci wa PSG kwallaye 51, daga cikin wasanni 58 da ya buga mata.