rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Afghanistan Taliban Ta'addanci Donald Trump

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojin Amurka zasu ci gaba da zama a Afghanistan bayan sulhu - Trump

media
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bazai janye dakarun kasar baki daya ba a kasar Afghanistan ko bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban rfi

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, kasar za ta ci gaba da ajiye dakarun sojinta akalla dubu 8 da dari 6 a Afghanistan ko da bayan kammaluwar yarjejeniyar zaman lafiyar da ake fatan kullawa tsakaninta da kungiyar Taliban.


Yayin wata tattaunawarsa da gidan Radiyon Fox, Donald Trump ya ce zasu bar dakarunsu dubu 8 da dari shida a cikin kasar ta Afghanistan ko da kuwa sun samu nasara a kokarinsu na ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya da mayakan Taliban.

A cewar Donald Trump ya zama wajibi Amurka ta ci gaba da barin dakaru a kasar saboda shirin ko ta kwana, yana mai gargadin cewa matukar kuma wani farmaki ya sake afkuwa kan dakarun na ta, to fa za ta kaddamar da runduna mafi karfi fiye da ta baya.

Kalaman na Trump dai ya fayyace bukatar da Amurka ke da shi wajen ganin ta kawo karshen yakin na Taliban wanda ya dauki kusan shekaru 20 ana gwabzawa, wanda kuma ake ganin shugaba Trump na son amfani da nasarar cimma yarjejeniyar a yakin neman zabensa cikin shekarar 2020.

Tun a bara ne Amurkan ke mabanbantan tattaunawa da Taliban don ganin an yi nasarar kulla yarjejeniyar da za ta kawo karshen yakin.

Yanzu haka dai akwai Sojin Amurka akalla dubu 14 da ke kasar ta Afghanistan adadin da ya yi matukar raguwa daga soji dubu 100 da Amurkan ta girke tun da farko.

Bugu da kari bukatar janye sojojin na daga cikin sharuddan da Taliban ta kafa kafin amincewa da kulla yarjejeniya da Amurkan.