rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bahamas Canjin Yanayi Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Guguwar Dorian na ci gaba da barna a Bahamas

media
Guguwar Dorian a Bahamas HO / NOAA/RAMMB / AFP

Rahotanni daga Bahamas na cewa mahaukaciyar guguwar Dorian da aka kwashe shekaru ba a ga makamanciyarta a tarihi ba, na ci gaba da tafka barna a yankin arewa maso yammacin kasar, inda ta haddasa mummunar ambaliyar ruwa tare da yaye rufin gine-gine.


Tun a ranar Lahadi, mahaukaciyar guguwar ta da ke gudun kilomita 285 a cikin sa'a guda ta afka wa kasar,  yayinda karfinta ya kai mataki na 5 kamar yadda masana yanayi suka tabbatar.

Tuni jami’an agaji suka bukaci dubban jama’a da su nemi mafaka a kwararan wurare, inda suka yi gargadin cewa, tsawon tozon guguwar daga sama zuwa kasa zai iya karuwa daga kafa 18 zuwa kafa 23.

A Amurka, tuni shugaba Donald Trump ya gana da tawagar jami’an bada agajin gaggawa ta kasar, tare da bada umarnin kwashe dubban jama’a daga yankunan gabar ruwa a Florida, daya daga cikin yankunan da masana suka yi hasashen cewa, guguwar ta Dorian za ta afkawa.

An ayyana dokar ta baci a jihohin Florida da Georgia da Arewaci da kuma Kudancin Carolina na Amurka.