rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Bahamas

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Adadin wadanda guguwar Dorian ta hallaka a Bahamas ya kai 43

media
Yankin da guguwar Dorian ta lalata a Bahamas. REUTERS/Dante Carrer

Rahotanni daga Bahamas na nuni da cewa adadin mutanen da kakkarfar guguwar Dorian ta hallaka ya kai 43 a safiyar yau Asabar dai dai lokacin da ake fargabar iya karuwar adadin bayan da jami’an agaji ke ci gaba da kai dauki kan baraguzan gine-gine.


Haka zalika sashen kula da guguwar ya ce akwai yiwuwar kara karfinta cikin daren yau, musamman a tsibirin Abaco yankin da ta ruguje gidaje 260.

Tun a ranar Lahadin da ta gabata kakkarfar guguwar wadda ke gudun kilomita 285 a cikin sa'a guda ta afka wa kasar, yayinda karfinta ya kai mataki na 5 kamar yadda masana yanayi suka tabbatar.

Jami’an agaji dai na ci gaba da gargadin jama’a da su nemi mafaka a kwararan wurare, inda suka yi gargadin cewa, tsawon tozon guguwar daga sama zuwa kasa zai iya karuwa daga kafa 18 zuwa kafa 23.