rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia

Amurka China Majalisar Dinkin Duniya Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka za ta kwato 'yancin musulmi 'yan kabilar Uighur na China

media
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Yuri Gripas

Kasar Amurka ta ce za ta yi amfani da taron Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a wannan watan wajen samarwa 'yan kabilar Uighur da ke fuskantar barazana daga gwamnatin China goyan bayan da ya dace.


Sakataren harkokin wajen Amurka mike Pompeo ya ce cin zarafin musulmi 'yan kabilar ta Uighur zai zama babban batun da za’a mayar da hankali akai, domin tabbatar da cewar sun samu cikakken 'yancin da ya dace.

Kasar Turkiya ce kadai daga kasashen Musulmi ke daga murya kan yadda ake cin zarafin 'yan kabilar ta Uighur Musulmi, sai kuma 'yan majalisun Amurka.

China dai na ci gaba da tsare dubun dubatar 'yan kabilar ta Uighur baya da ta zarge su da tayar da rikici, yayinda ta ke raba yara da iyayensu a wani mataki na sauya musu addini a bangare guda kuma mata da tsaffin kabilar ke fuskantar wulakantacciyar rayuwa.

Wannan dai ne karon farko da Amurkan a hukumance ta sha alwashin daukar mataki kan cin zarafin wanda ba tun yanzu ba kungiyoyin kare hakkin dan adam a lokuta da dama ke bayyana matakin China kan tsiraraun musulmin a matsayin mafi kololuwar cin zarafi.