rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta yi watsi da bukatar ganawa da Amurka bayan korar John Bolton

media
Shugaba Trump na Amurka da Shugaban Iran Hassan Rohani AFP

Sa’o’i kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da tube John Bolton mai ba shi shawarar kan sha’anin tsaro daga mukaminsa, Donald Trump ya ce a shirye ya ke ya gana da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ba tare da wani sharadi ba.


Kasar Iran ta yi watsi da bukatar Amurka na ganawa tsakanin shugaba Donald Trump da Hassan Rouhani a wajen taron Majalisar Dinkin Duniya da zai gudana a wannan wata a New York.

Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Majid Takht-Ravanchi yace Rouhani zai gana da Trump ne kawai idan Amurka ta kawo karshen ta’addancin kasuwancin da take yiwa kasar, wajen cire mata takunkumi.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da Sakataren Baitulmali Steven Mnuchin suka bayyana cewar shugaba Trump a shirye yake ya gana da shugaba Hassan Rouhani ba tare da gindaya sharudda ba, bayan ya kori mai bashi shawara kan harkokin tsaro John Bolton.

A watan jiya, shugaban Faransa Emmanuel Macron dake shiga tsakanin kasashen biyu, ya bayyana cewar akwai yiwuwar ganawa tsakanin bangarorin biyu.